Ayammacin ranar asabar ne 10/02/2018 wakilin kamfanin (MI FIT ) Dr Eliyas yakai ziyara gonar jami'a. Wannan kamfani na MI FIT  yana daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya dake sana'anta abubuwa da dama. Wakilin yasamu rakiyar Dr Salah Al'ajab ( me bada shawara a bangaren kiwon kaji), inda ya jagorance shi zuwa shashin 'yan tsaki ( kaji ) wanda aka kaddamar da kiwonsu a ranar juma'ar da tagabata. Mr Al'bariy Attayb ( shugaban gidan gonar) shine ya tarsu.