Mai girma mataimakin shugaban jami'a Dr Musa Daha Tayyillah ya isa farfajiyan jami'ar musulinci a Umbali na kasar Uganda, inda  mataimakin shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga Dr Halima ( daya daga cikin jigogin gudanarwa na jami'ar) da kuma wata tsohuwar dalibar jam'ar Afirikiyya mesuna Khadija.

Daga bisani sun samu damar  tattaunawa kan yadda za'a samar da  taimakekeniya atsakanin jami'o'in biyu. Wannan batu ya fito ne daga bakin Dr Abdul'aziz ( shugaban majalisar zartaswa na jami'ar) atare dashi akwai shugaban zartaswa na kungiyar addinin musulinci dake Uganda ( Dr Ibrahim Al'kazim ) da kuma Dr  Mustafa  Muh'd Aliy ( wakilin Isisco ).  Akarshe mai girma mataimakin jami'ar ta Afirikiyya ya mika kyaututtuka zuwa ga jami'ar ta musulinci.

A safiyar ranar Asabar 10/02/2018 awajan cigaba da bukukuwan nasu, mai girma mataimakin shugaban  jami’ar ta  Afirikiyya ya karbi kyautar girmamawa ga jami'ar ta Afirikiyya daga hannun maitamakin shugaban kasar Uganda