Sabon jakadan kasar turkiya Irfaan Nazir Ugulow ya ziyarci gidan gonar jami'a da Ailafun  asafiyar Asabar 10/02/2018. Inda shugaban jami'a prof Kamal Muh'd Ubaid da Mr Usama Marganiy Rashid ( me bada shawara ta musamman) da Mr Ja'afar Badiy da Mr Muh'd Abdurra'uf ( shugaban jin dadin dalibai) da shugaban kwalejin Noma da Kiwo ta jami'ar, da me kula da gidan gonan, da Mr As'sammaniy Al'hibr ( shugaban kungiyar manoma) da kuma sauran ma'aikatan jami'ar, duk suka tarbi wannan bako agidan gonar dake Al'ailafun.

Afarkon wannan ziyara, shugaban jami'ar yayiwa jakadan barka da zuwa. sannan yayi mishi cikakkan bayani akan gidan gonar na jami'ar da irin gudun muwar da gidan gonar ke bayarwa wajan ciyar da dalibanta na cikin jami'a. sannan yace : Jami'a ashirye take don karbar kowani  irin taimakekeniya atsakanin jami'ar da ofishin jakadancin na turkiya.

Anashi  bangaren, jakadan na kasar turkiya yayi matukar mamaki dangane da abubuwan da idanunshi suka gani agidan gonar. sannan ya bayyana kudirinshi na kulla alaka tsakanin jami'ar awannan bangare ( noma da kiwo) da jami'o'in turkiya don cigaban bangarorin biyu.

Har ila yau, jakadan yasamu daman halartan taron da mai girma shugaban jami'ar ta Afirikiyya ya shirya akan harkan noma. taron wanda akayishi don mika wasu makodan kudin akan aiyukan habbaka gidan gonan. Inda wanda alhakin wannan bangare yake kanshi ( Abdul'hak ) ya gabatar. Bayan haka kuma, shugaban jin dadin dalibai ( Mr Muh'd Abdurra'uf) yayi jinjina ga kasar ta turkiya wajan bada gudun muwanta na ciyar da daliban jami'ar.

Daga karshe jakadan ya jagoranci bude wani sabon shashi na Kaji masuyin Kwai.