Dr Musa Daha Tayyillah ( mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi) shida Mr Kamarul'anbiya  sun isa babban birnin Kampala na kasar Uganda domin halartar bikin da jami'ar musulinci dake kasar tashirya  adalilin yaye wasu dalibanta wanda  ya gudana a ranar Asabar 10/02/2018. Inda mai girma shugaban ( Al'hai'atul Al'kairiyya Al'islamiyya ) na kasar Mr Abdul'aziz Abkar ya tarbesu.

Dr Musa Daha yasamu damar ganawa da tsofaffin daliban jami'ar Afirikiyya dake kasar ta Uganda a yammacin ranar Alhamis.  Inda suka tattauna akan irin gudun mowar da kungiyar tasu ke bayarwa masamman abangaren ilimi, sannan kuma suka nema taimakon jami'ar ta Afirikiyya da tasanya musu hannu domin karfafa harka ilimi akasar tasu. Har ila yau daliban sun nema jami'ar ta Afirikiyya da takara musu wani adadi akan wanda take basu na daukan nauyin karatun dalibai akyauta wato ( scholarship) masamman a bangaren sakandare da kuma koyar da malamai abunda ya shafi limanci.

 

Anashi bangaren, mataimakin shugaban jami'ar ta Afirikiyya ya karfafa musu gwiwa akan bukatunsu da suka nema. Akarshi yayi godiya da irin tarbar da yasamu daga Mr Abdul'aziz Abkar.